rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Barack Obama

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Obama ya yi kakkausar suka kan siyasar Amurka

media
Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama REUTERS/Elizabeth Shafiroff

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya yi kakkausar suka a game da abin da yakira siyasar raba kawunan jama’a wadda wasu ke neman sake dawowa da ita kasar.


Obama, wanda ke gabatar da jawabi a taron yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar New Jersey a jam’iyyar Democrat, ya ce a yanzu muna karni na 21 ne, yayin da wasu ke kokarin mayar da siyasar Amurka tamkar karni na 19.

Wannan ne karo na farko da Obama mai shekaru 56 a duniya ya yi furuci a fagen siyasa tun bayan saukarsa daga karagar mulki a watan janairun da ya gabata.