Isa ga babban shafi
Sahel

Taron Majalisar Dinkin Duniya don tallafa wa rundunar Sahel

A wannan litinin, Faransa na jagorantar wani taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York don tafka mahawara kan yadda za’a samu kudaden tafiyar da rundunar sojin da za ta yaki da ‘yan ta’adda da masu aikata sauran laifufuka a Yankin Sahel, rundunar da Amurka ke nuna shakku dangane da kafuwarta.

Yankin Sahel
Yankin Sahel RFI
Talla

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ne ke jagoranctar taron da zai goya wa rundunar sojojin da suka fito daga kasashen Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritania da kuma Nijar baya.

Faransa na bukatar ganin masu ba da agaji sun yunkura, yayin da ita kuma Majalisar Dinkin Duniya za ta bayar da gudumawar kayan aiki da kudaden da suka dace domin ganin rundunar ta fara aiki cikin kwanaki masu zuwa.

Ita Amurka na cewa, duk da ya ke tana shirin ba da gudumawa, bai dace Majalisar Dinkin Duniya ta sanya hannu a cikin rundunar ba, matsayin da Faransa da kawayenta suka ki amincewa da shi.

Jakadiyar Amurka a Majalisar, Nikki Haley ta rubuta wa Babban Magatakarda na Majalisar cewa har yanzu matsayinsu kan tallafa wa rundunar bai sauya ba.

Sakatare Janar Antonio Guterres ya bayyana cewar kafa rundunar wata dama ce da za ta taimaka wajen samar da tsaro a Yankin na Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.