Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Miliyoyin yara mata na fuskantar fyade-UNICEF

Majalisar dinkin duniya ta ce akalla yara mata guda miliyan 15 ne a fadin duniya ake cin zarafinsu ta hanyar fyade.

Miliyoyin yara ne ke fuskantar cin zarafi a fadin duniya.
Miliyoyin yara ne ke fuskantar cin zarafi a fadin duniya. REUTERS/Siegfried Modola
Talla

Majalisar ta bayyana haka ne a cikin wani rahoto da hukumar kula da kananan yara ta duniya UNICEF ta bayar, bayan yin nazari a kan bayanai da suka fito daga kasashe 40.

Rahoton ya ce Kamaru ita ce kasar da ta fi kowace kasa fama da wannan matsala, inda ake tursasa ma yarinya daya daga cikin shida saduwa ba tare da son ransu ba.

Kungiyar ta UNICEF ta ce duk da yawaitar matsalar ta cin zarafin yara mata, daya ne kacal daga cikin dari na irin wadanda abin ke faruwa da su suke neman taimako.

Sannan ta kara da cewa yawanci matsalar tana tasowa ne daga wadanda suke tare da yaran, musamman ma ‘yan’uwa, da abokai, da mazajen aurensu ko kuma abokan karatu.

UNICEF din ta ce yawaitar wannan matsala da ta shafi yara mata zai iya kawo cikas ga cigaban duniya, musamman ma yunkurin da ake yi na tabbatar da dorewar kudurorin muradun karni, wanda zai kawo karshen talauci, da yunwa, da daidato tsakanin mata da maza da kuma kare daukacin duniya, nan da shekara ta 2030.

Rahoton ya kuma nuna cewa akwai yiwuwar yawan yara mata da ke fuskantar wannan matsala ta fyade ka iya fin miliyan 15, kasancewar da yawa daga cikin wadanda hakan ke faruwa da su ba su iya kai rahoto, sannan kuma akwai kasashe da dama wadanda ba a samu nasu cikakken bayanin ba.

Sai dai hukumar ta ce samar da dokoki wadanda za su kare yara, da kuma tallafi daga bangarorin kula da walwalar al’umma za su iya kawo sauyi a al’amarin.

Wadda ta wallafa rahoton, Claudia Cappa ta ce an gano cewa yin aiki tare da gwamnatoci domin samar da matakai ta bangarori daban-daban, kamar bangaren ilimi da shari’a ya na haifar da ‘da mai ido.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.