rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Iraqi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane sama da 213 suka mutu a Iran da Iraqi

media
Girgizar kasa ta rusa gidaje a DarbandikhanIrak A Iraqi TWITTER - Osama Golpy/Rudaw/Social Media/via REUTERS

Akalla mutane 213 aka tabbatar da mutuwar su sakamakon wata girgizar kasar da aka samu mai karfin maki sama da 7 akan iyakar kasashen Iran da Iraqi.


Rahotanni daga Arewacin Iraqi sun nuna yadda mutane suka yi ta ficewa daga gidajen su suna neman mafaka a Sulaimaniyah, yayin da girgizar kasar ta rusa gidaje a Darbandikhan.

Gidan talabijin din Iran ya ruwaito cewar mutane 213 suka mutu a hadarin, yayin da Kamfanin dillancin labaran kasar ya ce mutane sama da 1700 sun jikkata.

Mojtaba Nikkerdar, mataimakin Gwamnan Kermanshah, yace sun kafa kwamitoci domin gudanar da aikin jinkai ga wadanda hadarin ya ritsa da su.

Shugaban hukumar agajin gaggawa na Iran, Pir Hossein Koolivand ya ce yana da wahala a tura masu ma’aikantan aikin jinkai a kauyuka saboda lalacewar hanyoyi.