rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Iraqi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutanen da suka mutu sun haura 400 a Iran da Iraqi

media
Girgizar kasar ta shafi al'umma a Iran da Iraq. Tasnim News Agency/REUTERS

Jami’an agaji na cigaba da kokarin ceto wadanda suka tsira da rayukansu bayan girgizar kasar da ta jijjiga yankunan arewacin iyakar kasashen Iraqi da Iran.


Kamfanin dillancin labaru na Iran ya ce ya zuwa yanzu mutane sama da 407 ne aka tabbatar da cewa sun hallaka a girgizarkasar mai karfin maki 7.3.

Baya ga mutane, da hasarar daruruwa rayukan da aka samu, jami’an ceto sun ce yawan wadanda suka jikkata, ya zarce 7,000, a girgizar kasar da ta zama mafi muni da aka taba gani cikin wannan shekara ta 2017.

An dai fi samun hasarar rayukan ne a yammacin lardin Kermanshah da ke kasar Iran inda a nan kawai mutane 300 ne suka hallaka, inda jami’an ceto suka gaza isa gare su cikin sauki sakamakon zaftarewar kasar da girgizar kasar ta haifar.

Daga bangaren kasar Iraqi kuwa sama da mutane 10 jami’ai suka tabbatar da mutuwarsu, inda girgizar kasar ta fi shafar garin Darbandikhanda yankin Kurdistan.