Isa ga babban shafi
Iran

Ana zaman makoki a Iran bayan girgizar kasa

Masu aikin agaji na ci gaba da kai dauki ga wadanda hadarin ya ritsa da su da kuma fatar samun wasu da burabuzai suka bine da ran su.Wannan girgizar kasar na a matsayin daya daga cikin mafi munin da Iran ta gani.

Wasu unguwanni da lamarin girgizar kasa ta shafa  a Iran
Wasu unguwanni da lamarin girgizar kasa ta shafa a Iran Farzad MENATI / TASNIM NEWS / AFP
Talla

Shugaban addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya umurci daruruwan motocin daukar marasa lafiya da jiragen saman soji masu saukar unglu su taimaka wajen ceto wadanda hadarin ya shafa.

Tuni gwamnatin kasar ta bayyana yau talata a matsayin ranar zaman makoki saboda rasa mutanen sama da 400 cikin su harda mutane 280 daga garin Sar-e Pol-e Zahab, yayin da sama da 6,700 suka jikkata, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta sanar.

Shugaban zaratan sojin Iran, Manjo Janar Mohammad Ali Jafari yace abinda mutane ke bukata cikin gaggawa shine ruwan sha da tantunan da zasu tsuguna a cikin su da kuma abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.