wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa
Sama da mutane miliyan 425 na fama da cutar sukari - WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce daya daga cikin mutane 11 da shekarunsu suka haura 20 a duniya na fama da cutar sukari wato diabetis. Ranar Talata hukumar lafiya ta duniya ta kebe, domin yaki da cutar, inda aka bayyana adadin masu fama da ita a sassan duniya da cewa sun kai milyan 425. Wakilinmu a Agadez da ke Jamhuriyar Nijar Umaru Sani, ya yi nazari kan yadda masu dauke da cutar ke fama da rashin magani ko kuma kwararrun likitoci domin lura da su a rahotonsa.