Isa ga babban shafi
Myanmar

Sojin Myanmar sun yi matan Rohingya fyade- HRW

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch ta ce, sojojin gwamnatin Myanmar sun yi wa mata da dama daga kabilar Rohingya Musulmi fyade a lokacin da suka kai samame yankunansu, abin da ya tilasta wa dubban matan tserewa zuwa Bangladesh.

Wasu daga cikin 'yan matan kabilar Rohingya Musulmi da ke samun mafaka a Bangladesh
Wasu daga cikin 'yan matan kabilar Rohingya Musulmi da ke samun mafaka a Bangladesh REUTERS/Adnan Abidi
Talla

Wani rahoto da kungiyar ta Human Rights Watch ta fitar a yau, ya nuna cewar sojojin gwamnatin Myanmar sun aikata laifufukan yaki ta hanyar fyade da kuma azabtar da 'yan kabilar Rohingya da kuma hallaka wasu daga cikin su.

Kungiyar ta ce, ta tattara wadannan bayanai ne bayan tambayoyin da ta yi wa mata da 'yan matan da aka yi wa fyaden da kungiyoyin agaji da kuma hukumomin lafiyar da suka kula da su a Bangladesh.

Skye Wheeler, wani mai bincike a kungiyar da ya rubuta wannan rahoto ya ce, wannan aika-aika da sojojin suka yi wa wadannan mata ya jefa su cikin rudani da  fargaba.

Rahotan ya ce, daga cikin mata 29 da aka tambaya, guda daya ce kawai ta ce ba sojoji da yawa ne suka yi lalata da ita ba, yayin da wasu suka ce da idonsu suka ga lokacin da ake kashe mazajensu da kuma 'ya'yansu.

Tuni kasashen duniya suka yi Allah- wadai da abin da ya faru, yayin da aka bukaci gudanar da bincike domin hukunta wadanda ake zargi da aikata laifufukan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.