rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

EU ta gargadi Birtaiya game da kurewar lokacin ficewarta

media
Shugaban Hukumar Tarayyar turai, Jean-Claude Juncker a zauren taronsu a Gothenburg na Sweden TT News Agency/Jonas Ekstromer/via REUTERS

Shugabannin Kasashen Turai da ke gudanar da taro a Sweden sun gargadi Firaministar Birtaniya Theresa May game da kurewar lokacin cimma yarjejeniyar ficewar kasar daga Tarayyar Turai.


Shugabanin kasashen Turan sun yi gargadin ne a yayin da ake fargabar cewa, kokarin shiga zangon gaba nan da watan Disamba don ci gaba da tattaunawar ficewar Birtaniya, zai sukurkuce.

Zancen ficewar Birtaniyar ne dai ya mamaye taron da shugabannin na Turai ke gudanarwa yanzu haka a birnin Gothenburg na Sweden, amma duk da haka za su tattanawa kan wasu batutuwa daban da suka hada da inganta jin dadin rayuwar jama’a da kuma barazanar zazzafan ra’ayin siyasa bayan ficewar kasar.

Firaministar Birtaniyar Theresa May ta bayyana kwarin gwiwar cewa, kungiyar ta EU za ta mayar da martini mai dadi bayan ganawarta da shugabannin kungiyar daya bayan daya a kebe.

Sai dai dukkaninsu sun gargade ta cewa, lallai lokacin tattauna kan batutuwan ficewar kasar na kurewa.

Shugaban Hukumar Tarayyar Turai Jean Claude Juncker ya ce, yana fatan za su cimma matsaya dangane da ficewar a taron da za su gudanar a cikin watan Disamba amma a cewarsa, akwai jan aiki a gaba.

A makon jiya ne wakilin Birtaiya a tattauawar ficewar, Michel Barnier ya gargadi cewa, kasar na da makwanni biyu da suka rage ma ta na cika sharuddan ficewarta daga EU.