rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Lebanon Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hariri zai koma Lebanon a makon gobe

media
Firaministan Lebanon mai murabus Saad Hariri tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron a fadar gwamnatin Faransa ta Elysée REUTERS/Gonzalo Fuentes

Firaministan Lebanon mai murabus Sa’ad Hariri ya bayyana cewa, zai koma birnin Beirut nan da kankanin lokaci don halartar bikin ranar samun ‘yancin kasar a ranar Laraba mai zuwa.


Wannan na zuwa a yayin da kasar ta  fada  cikin rikicin siyasa tun bayan da ya sanar da matakinsa na yin murabus a Saudiya.

Hariri ya sanar da shirinsa na komawa Lebanon ne bayan ganawarsa da shugaban Faransa Emmanuel Macron a birnin Paris a yau Asabar.

Mr. Hariri ya kara da cewa, zai taka rawa a bikin samun ‘yancin kan kasarsa, sannan kuma zai sanar da matsayarsa akan lamurran siyasar kasar bayan ganawar da zai yi da shugaba Michel Aoun.

Shugaban Faransa Emmanuel Macrona na kokarin samar da matsalaha ce game da rikicin siyasar Lebanon.