rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iraqi Syria ISIL Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dakarun Iraqi sun kaddamar da farmakin murkushe ISIS

media
Wasu daga cikin dakarun da ke yaki da mayakan ISIS REUTERS/Rodi Said

Dakarun Iraqi sun kaddamar da gagarumin farmaki da nufin kakkabe sauran mayakan ISIS a yankin yammacin Sahara da ke kusa da kan iyakar Syria.


Dakarun na Iraqi sun kunshi sojoji da jami’an ‘yan sandan tarayya da wata runduna ta musamman da ake kira Hashed al-Shaabi.

Wata sanarwa da shugaban dakarun na hadaka ya fitar, Janar Abdelamir Yarallah ta ce, a wannan safiya ta Alhamis ne aka fara aikin murkushe mayakan na ISIS a yankin Al-Jazeera da ke kusa da lardunan Salaheddin da Ninevah da kuma Anbar.

A ranar Talata ne ne Firaminista Iraqi ya sanar cewa, an murkushe mayaka ISIS ta fannin karfin soji, yayin da ya ce, zai sanar da nasara ta karshe da zaran an kammala murkushe su baki daya a yankin Sahara.

A ranar Juma'a ne dakarun suka karbe birnin Rawa, wanda ya kasance tunga ta a hannun ISIS.

Rikicin ISIS ya yi sanadiyar mutuwar dubun dubatan mutane a Iraqi da Syria, yayin da miliyoyi suka rasa muhallansu, lamarin da ya tsananta matsalar kwararar 'yan gudun hijira a kasashen Turai.