Isa ga babban shafi
Rasha-Syria

Taron Rasha zai kawo karshen rikicin Syria- Erdogan

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya ce, yana da kwarin gwiwa ka cewa taron da aka gudanar a Rasha a jiya Laraba da ya samu halartar takwarorinsa na Iran Hassan Rouhani da na Rasha Vladmir Putin, zai taka rawa wajen kawo karshen zubar da jini a Syria.

Shugaba Hassan Rouhani na Iran da na Rasha, Vladmir Putin da kuma na Turkiya, Recep Erdogan
Shugaba Hassan Rouhani na Iran da na Rasha, Vladmir Putin da kuma na Turkiya, Recep Erdogan © Reuters
Talla

Ba kasafai aka saba ganin haduwar shugabannin kasashen uku ba a lokaci guda, wato na Rasha da Iran da ke goyon bayan shugaban Syria Bashar al-Assad da kuma shugaban Turkiya da ke taimaka wa ‘yan tawayen Syria.

Yayin gabatar da jawabi bayan bude taron a Sochi da ke Kudancin Rasha, shugabannin sun sha alwashin tabbatar da cimma burin kawo karshen yakin Syria, musamman idan aka yi la’akari da yadda suka yi nasarar murkushe mayakan kungiyar IS a yankunan kasar da suka mamaye a can baya.

A farkon wannan makon ne shugaban Rasha Vladmir Putin ya karbi bakwancin shugaban Syria Bashar al-Assad a birnin na Sochi kuma a karo na farko kenan da shugaban ya yi baluguro zuwa wajen Syria bayan makamanciyar ziyarar da ya kai Rashan shekaru 2 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.