Isa ga babban shafi
Syria

Fiye da fararen hula 45 sun mutu a harin Rasha da Syria

Wasu tagwayen hare-hare ta sama da jiragen yakin Rasha suka kai yankin Dier Ezzor na Syria ya hallaka akalla fararen hula 34, adai dai lokacin da dakarun sojin Syria suka hallaka wasu karin fararen hular 23 sakamakon bama-baman da suka jefa a yammacin Ghouta yankin da ke hannun ‘yan tawayen kasar.

Fiye da mutum dubu dari uku da raba’in ne suka mutu tun bayan fara yakin basasar Syria a shekarar 2011.
Fiye da mutum dubu dari uku da raba’in ne suka mutu tun bayan fara yakin basasar Syria a shekarar 2011. REUTERS/Rodi Said
Talla

Tunda sanyin safiya ne Jiragen na Rasha a cewar hukumar kare hakkin dan adam da ke Syrian suka fara luguden wuta a kauyen al’shafah da ke gabashin yankin Dier Ezzor.

A cewar hukumar bisa ga dukkanin alamu da yanayin jirgin tana da tabbacin jiragen yakin Rasha ne suka kaddamar da hare-haren a yankin da yake shi ne na karshe a hannun Mayakan IS na kasar ta Syria.

A bangare guda suma sojin Syriar a harin da suka kaddamar a gabashin Ghota da ke wajen birnin Damascus yankin da ke hannun ‘yan tawayen kasar wadanda ke samun goyon bayan Turkiyya sun hallaka kimanin mutum 23 baya ga jikkata da dama.

Tun a shekarar 2015 ne gwamnatin shugaba Bashar al-assad ta samu goyon bayan gwamnatin Rasha wajen fatattakar mayakan IS da ‘yan tawaye daga birnin Damascus wanda kuma ya haddasa hallaka fararen hula da dama.

Fiye da mutum dubu dari uku da raba’in ne suka mutu tun bayan fara yakin basasar Syria a shekarar 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.