Isa ga babban shafi
Korea ta arewa

Korea ta Arewa ta yi sabon gwajin makami mai linzami

Kasar Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzami wanda shine irin sa na farko a cikin watanni biyu. Babban hafsan sojin Koriya ta kudu yace makamin ya tashi ne daga gabashin birnin Pyongyan, yayin da ma’aikatar tsaron Amurka ta ce taji rugugin harba makamin.

Kim Jong Un shugaban kasar Korea ta Arewa
Kim Jong Un shugaban kasar Korea ta Arewa KCNA/File Photo via REUTERS
Talla

Wannan dai shine gwaji na farko tun ranar 15 ga watan Satumba, kuma yana zuwa ne mako guda bayan Amurka ta sake sanyawa kasar karin takunkumi.

A watan Satumba sau 6 Koriya ta Arewa ke gwajin makamai daban daban duk da haramcin da Majalisar Dinkin Duniya tayi a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.