Isa ga babban shafi
AU-EU

Shugabannin Afrika da Turai na taro a Abidjan

A yau laraba ake gudanar da taron koli karo na biyar da ya hada shugabannin kasashen Turai da na Afrika a birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire.

Shugabar Jamus Angela Merkel tare da wasu shugabannin Afirka a wurin taron AU-EU a Abidjan
Shugabar Jamus Angela Merkel tare da wasu shugabannin Afirka a wurin taron AU-EU a Abidjan REUTERS/Luc Gnago
Talla

Wakilai sama da dubu biyar daga kasashe da kuma kungiyoyi akalla 80 ne ke halartar taron da zai mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi matasa a wannan zamani.

Daga cikin abubuwan da taron zai mayar da hankali sun hada da matsalar rashin aikin yi da ta’addanci da kuma kwararar ’yan gudun hijira  daga Afrika zuwa Turai

Masu hannu da shuni a taron sun bayyana fargabarsu kan yadda ake ci gaba da samun karuwar al’umma a nahiyar Afrika ba tare da wani tanadi na musamman da zai inganta rayuwarsu ba.

Alkaluma sun nuna cewa, nan da shekarar 2050, yawan mutanen Afrika zai kai biliyan 2.4, abin da ya sa ake ganin wajibi ne a samar da isassun guraben ayyukan yi ga matasan da za su zo nan gaba.

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Antonio Tajani ya ce, matukar aka gaza samar da guraben ayyukan ga matasan, hakan ka iya jefa su cikin miyagun dabi’u.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.