rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Emmanuel Macron Iraqi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Macron na neman shiga tsakani a rikicin Kurdawan Iraqi

media
Shugaba Emmanuel Macron ya kuma bukaci a bashi dama don shiga tsakanin gwamnatin ta Iraqi da bangaren Kurdawan da nufin kawo karshen takaddamar. REUTERS/Etienne Laurent/Pool

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci gaggauta fara tattaunawa tsakanin gwamnatin Iraqi da Kurdawan da suka nemi kafa kasa mai cin gashin kanta.


Da ya ganawa da Firaministan yankin Nachervan Barzani da mataimakinsa Quobad Talabani, Macron ya bukaci tattaunawa ta fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu domin kawo karshen matsalar da ke tsakaninsu.

Baraka ta fito fili tsakanin yankin na Kurdawa da gwamnatin Iraqin ne baya da yankin ya kada kuri'ar raba gardamar ballewa daga kasar, Lamarin da ya sa gwamnatin kasar daukar tsauraran matakai don kaucewa ballewar yankin.

Shugaba Macron ya yi tayin neman damar shiga tsakani don kawo karshe matsalar.