rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Somalia Chadi Yemen Libya Syria Iran ‘Yan gudun Hijira

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun Koli ta goyi bayan hana Musulmai shiga Amurka

media
Da dama daga cikin Amurkawa na adawa da matakin haramta wa kasashen Musulmi shiga Amurka REUTERS/Tom Mihalek

Kotun kolin Amurka ta bai wa gwamnati damar fara aiki da kudurin dokar da ke hana wa ‘yan asalin wasu kasashe 6 na Musulmi damar shiga kasar kafin yanke hukunci dangane da karar da wasu jihohi suka daukaka a wannan batu.


Matakin dai ya shafi kasashen Chadi da Syria da Yemen da Iran da Somalia da kuma Libya, wadanda Amurka ta bayyana a matsayin masu hatsari ga makomar tsaronta.

Alkalai bakwai daga cikin tara a kotun sun janye hukuncin da wata karamar kotu ta yanke na dakatar da gwamnatin Amurka daga aiwatar da dokar haramta wa kasashen na Musulmin shiga kasar.

Sai dai a wannan makon ne kotunan daukaka kara na tarayya da ke Francisco na California da Richmond na Virginia za su yi zaman sauraren korafi kan matakin da kotun kolin ta dauka.