Isa ga babban shafi
Amurka-Falasdinu

'Amurka ba za ta yi jagorancin sulhun rikicin Gabas ta Tsakiya ba'

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya bayyana cewa Amurka ba za ta ci gaba da jagorancin shirin sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya ba sakamakon bayyana Birnin Kudus a matsayin babban birnin Israila.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas REUTERS/Carlos Barria
Talla

Sakatare Janar na kungiyar Falasdinu Saeb Erakat ya ce matakin Trump ya rusa duk wani shirin samun kasashe biyu tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

Kungiyar Hamas ta ce matakin zai bude kofar jahannama ga Amurka da manufofin ta a Yankin.

Ita kuwa Iran cewa ta yi matakin zai bude wata kofar fara intifada.

Shi kuwa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yabawa shugaba Trump kan abinda ya kira jawabin da ya yi mai dimbin tarihi.

A cewar Netanyahu babu zaman lafiya muddin ba a sanya birnin Kudus a matsayin babban birnin Israila ba tare da kira ga daukacin kasashen da ke son zaman lafiya da su bi sahun Amurka wajen mayar da ofishin Jakadancin su can.

Netanyahu ya kuma mika godiyarsa ga Trump da daukan wannan mataki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.