Isa ga babban shafi
amurka-syria

Amurka na shakku kan matakin Rasha a Syria

Ma’aikatar tsaron Amurka, Pentagon ta bayyana shakkunta kan sanarwar da Rasha ta bayar ta janye mafi yawan dakarunta daga kasar Syria.

Shugaban Syria Bashar al Assad da takwaransa na Rasha, Vladmir Putin da Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu a Syria
Shugaban Syria Bashar al Assad da takwaransa na Rasha, Vladmir Putin da Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu a Syria Sputnik via REUTERS
Talla

Kakakin ma’aikatar tsaron, Kwamanda Adrian Rankine-Galloway ya bayyana cewa, sanarwar da Rasha ta bayar ta rage yawan dakarunta daga kasar Syria ba za ta shafi muradun Amruka a Syria ba.

Kakakin ma’aikatar tsaron ya kara da cewa, rundunar haɗakar dakarun ƙasashen duniya da Amurka ke jagoranta wajen yaki da ‘yan ta’adda a Syria za ta ci gaba da bai wa mayakan ‘yan tawaye goyon bayan da ta ke ba su ba tare da kasala ba.

A jiya Litanin ne shugaban Rasha Vladimir Putin a wata ziyarar ba-zata da ya kai Syria, ya bada umarnin janye wani bangare mai yawa na dakarun Rasha da ke Syria, ‘yan kwanaki bayan da Rashar ta bada sanarwa kawo karshen daular da kungiyar ISIS ta ce ta kafa a Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.