Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya ja hankalin Trump kan ɗumamar yanayi

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tunatar da takwaransa na Amurka Donald Trump game da sauke nauyin da ya rataya a wuyansa bayan ya janye ƙasarsa daga yarjejeniyar ɗumamar yanayi da aka cimma shekaru biyu da suka gabata a birnin Paris.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na karbar bakwancin shugabannin kasashen duniya 50 a birnin Paris a taron sauyin yanayi
Shugaban Faransa Emmanuel Macron na karbar bakwancin shugabannin kasashen duniya 50 a birnin Paris a taron sauyin yanayi REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da shugabannin ƙasashen duniya 50 ke halartar taro a birnin Paris a wannan Talata don tattauna kan batutuwan da suka shafi sauyin yanayi.

A yayin zantawa da gidan talabijin na CBS gabanin bude taron na yau, shugaba Macron ya yi wasti da batun cewa, Trump zai iya cimma matsaya kan wata sabuwar yarjejeniyar sauyin yanayi.

Macron ya ce, bai shirya sake kulla wata sabuwar yarjejeniya ba kamar yadda Trump ke fata, amma a shirye yake ya yi wa Trump maraba da dawowa cikin tsohuwar yarjejeniyar.

Macron ya kara da cewa, shugaba Trump zai sauya matsayinsa kan yarjejeniyar ta Paris nan da wasu watanni ko shekaru masu zuwa.

Taron na wannan Talata na a matsayin yunkuri domin cike giɓin da ficewar Amurka ta haddasa musamman kuɗaɗen da aka yi hasashe, in da Macron ya sanar da ware Euro milyan 35 a matsayin gudunmuwar Faransa a asusun da aka kafa domin tunkarar wannan matsala ta sauyin yanayi.

Bayan sanar da ware wadannan kuɗaɗe a cikin watan yunin da ya gabata, Macron ya roki masana da masu bincike daga kowane bangare, da su bayar da tasu gudunmuwa a wannan yunkuri da ake yi da nufin ceto duniya daga matsalolin sauyin yanayi.

A rana makamanciyar wannan ce ƙasashen duniya 195 suka sanya hannu kan yarjejeniyar rage ɗumamar yanayi, to sai dai matakin da Trump ya dauka na janye Amurka daga yarjejeniyar, lamari ne da ya haddasa fargaba a zukatan jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.