Isa ga babban shafi
Amurka

Matashi ya tayar da bam a birnin New York

Wani matashi mai shekaru 27 ya tayar da abin fashewar da ya yi damara da shi a wata babbar tashar jiragen ƙasa ta ƙarƙashin ƙasa da ke birnin New York na Amurka, abin da ya raunata mutane uku.

Jami'an kashe gobara sun halarci wurin da harin ya faru a birnin New York
Jami'an kashe gobara sun halarci wurin da harin ya faru a birnin New York 路透社。
Talla

Hakan na zuwa ne makwanni 6 da wani matuƙi ya yi amfani da babbar motar a-kori-kura ya mutsuke mutanen da ke tafiya a gefen hanya a birnin.

Magajin garin New York, Bill de Blasio ya bayyana harin da yunkurin ta’addanci.  Akayed Ullah.

Ita dai tashar jiragen da aka kai wa harin ba ta da nisa da shahararren dandalin Times Square, kuma al’amarin ya haifar da dimuwa tsakanin matafiya.

Gwamnan jihar New York Andrew Cuomo ya shaida wa manema labarai cewa, akwai mutane da yawa masu kokarin ganin sun kai wa birnin hari, musamman ma makiya ‘yanci da kuma mulkin demokradiyya.

Maharin mai suna Akayed Ullah ya samu rauni a wasu sassan jikinsa bayan tashin abin fashewar.

A karshen watan Oktoba ne wani mahari dan asalin kasar Uzbekistan ya karkata akalar motar da yake tukawa kan matafiya da mahaya Babura a New York, in da ya hallaka mutane 8 tare da jikkata 12.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.