Isa ga babban shafi
Rasha

Tattaunawar Amurka da Korea ta Arewa ta dace- Putin

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya yaba kan yadda Amurka ta fahimci cewa, ya dace ta tattauna da Korea ta Arewa wadda ta yi wa Amurka barazanar harin nukiliya.

Shugaban Rasha Vladmir Putin a yayin taron manema labarai a birnin Moscow
Shugaban Rasha Vladmir Putin a yayin taron manema labarai a birnin Moscow REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Mr. Putin ya bayyana haka ne a yayin gudanar da taron manema labarai a wannan Alhamis, wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da shugaban ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takara don neman sabon wa’adin shekaru shida.

Duk da dai shugaba Putin ya jinjinawa takawaransa na Amurka Donald Trump kan salon jagorancinsa, amma ya musanta zargin da aka dau lokaci ana yi wa Rasha na kutse a zaben 2016 a Amurka.

Kazalila shugaban ya ce, ‘yan adawar kasar na fatan juyin mulki, amma ya yi gargadi game da tashi hankali a kasar.

Putin ya jaddada aniyarsa ta sake tsayawa takara, in da ya ce, a wannan karo zai fito ne a matsayin dan takara mai cin gashin kansa ba tare da neman goyon bayan jam’iyyara ba.

Tun a shekarar 1999 ne, Putin ke mulki a Rasha, yayain da ya ke shirn zama shugaban kasar mafi dadewa kan karaga bayan Joseph Stalin.

A bangare guda shugaba Putin ya ce, Rash aba za ta amince da abin da ya kira salon juyin mulkin Ukraine ba.

Mr. Putin ya kuma tabo batun zargin da ake yi wa ‘yan wasan Rasha na kwankwadn kwayoyin kara kuzari, abin da ya sa hukumar wasanin Olympics ta duniya ta harama kasar shiga gasar da za a gudanar a badi.

A cewar Putin a shirye yake ya kare ‘yan wasan da ake zargi a gaban kotu, duk dai ya ce, kotun ka iya hada kai da hukumar wasannin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.