"An samu raguwar rasa rayukan 'Yan Jaridu a 2017"
Rahoton da kungiyar kare hakkin ‘Yan Jaridu ta Reporters Sans Frontieres ta fitar a wannan Talata, ya ce an kashe ‘Yan Jaridu da sauran ma’aikatan yada labarai 65 a sassan duniya cikin shekara ta 2017 da ke gaf da kawo karshe.
Wallafawa ranar:
Kungiyar ta ce rahoton, na nuni da cewa shekarar bana an samu karancin rasa rayukan ‘yan jarida, idan aka kwatanta da sauran shekaru 14 da aka shafe na baya-bayan nan.
Rahoton ya danganta samun rangwamen hasarar rayukan ‘Yan Jaridun, da yadda ma’aikatan yada labarai suka janye daga mafi yawan kasashen da ke fama da tashe-tashen hankula.
Har yanzu dai Syria ce kasa mafi hadari ga ma’aikatan kafafen yada labarai, inda a wannan shekara ‘Yan Jarida 12 suka hallaka, sai kuma kasar Mexico inda aka hallaka ‘Yan Jarida 11 a wannan shekara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu