Isa ga babban shafi

Mutum Milyan guda na fama da cutar Kwalara a Yemen

Kungiyar agajin kasa da kasa ta Red Cross ta ce Adaddin mutanen da ke dauke da cutar kwalara a Kasar Yemen yanzu haka ya kai kimanin mutum miliyan guda, a dai dai lokacin da al’ummar kasar ke ci gaba da cin gurbatattun abinci da ruwan sha sakamakon yakin da ya tagayyara su.

Akalla mutum Milyan guda ke fama da cutar Kwalara a Yemen sanadiyyar rufe Iyakokin da za a shigo abinci da magunguna sakamakon yakin da ake ci gaba da fafatawa.
Akalla mutum Milyan guda ke fama da cutar Kwalara a Yemen sanadiyyar rufe Iyakokin da za a shigo abinci da magunguna sakamakon yakin da ake ci gaba da fafatawa. REUTERS
Talla

Ko a watan Nuwamban da ya gabata ma sai dai Hukumar Lafiya ta duniya, WHO, ta fitar da wata sanarwa da ke gargadin cewa fiyeda mutum dubu biyu sun mutu sanadiyyar Kwalarar.

Wata kungiya ta MSF da ke bayyana takaicinta dangane da wannan alkallumar, ta ce kin daukan matakan gaggawa ka iya kara yawan mutanen da cutar za ta ci gaba da kashewa a kowacce rana.

Yemen dai yanzu haka na ci gaba da fuskantar yaki baya ga rufe mata iyakokin lamarin da ya hana shigo mata da abinci da magaunguna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.