Isa ga babban shafi
Indonesia

Dutse ya yi aman wuta mafi muni cikin 2017 a Indonesia

Mahukunta a Indonesia sun ce aman wuta da tsaunin Sinabung ya yi a ranar Laraba shi ne mafi muni a wannan shekara ta 2017 a ƙasar.

Dutsen Mount Agung da ya yi aman wuta a Indonesia.
Dutsen Mount Agung da ya yi aman wuta a Indonesia. REUTERS/Petra Simkova
Talla

Ya zuwa yanzu tsaunin ya yi sanadiyyar raba mutane sama da 3,000 da muhallansu tun bayan da ya dawo da yin aman wuta a shekara ta 2010, bayan kwashe kimanin shekaru 400 ba tare da ya yi aman wuta ba.

Aman wuta da dutsen ya yi na ranar Laraba ya turnniƙe sararin samaniya da kuma harabar yankin da toka, wanda ya yi sanadiyyar lalacewar amfanin gona mai yawa.

A watan Fabrairun shekara ta 2017, dutsen ya yi amai wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 16.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.