Isa ga babban shafi

Kasashen duniya na bukukuwan shiga sabuwar shekara

Milyoyin al’ummar duniya sun shafe daren jiya zuwa safiyar yau suna bukukuwan shiga sabuwar shekarar tare da gudanar da shagulgulan masu kayatarwa da suka hada da wasan wuta a sassa daban-daban na duniya.

Bukukuwan Sbauwar shekara a birnin Paris
Bukukuwan Sbauwar shekara a birnin Paris Lionel BONAVENTURE / AFP
Talla

Kasashen Australia da Hong Kong ne suka fara shiga sabuwar shekarar, inda mawaka da al’ummar kasashen suka yi ta amfani da kayan wuta domin nuna murnar su da wannan shekara ta 2018.

A kasashen Turai kuwa an tsaurara matakan tsaro, musamman a birnin Paris na kasar Faransa inda aka girke jami'an tsaro dubu 2, daga cikin jami’an tsaro dubu 140 da aka girke a sassan kasar.

A Philippines mutane kusan 200 suka jikkata a shagulgulan wasan wuta da aka yi, don murnar shiga wannan shekarar, duk da cewa shugaban kasar Rodrigo Duterte ya haramta ji ko ganin an yi wannan wasan.

Tun a watan shida na shekarar da ta gabata ne aka kafa doka a kasar don hana wasan wuta da aka saba yi duk shekara saboda asarar rayukan jama’a da ke biyo baya.

A wannan kasa da makwabciyarta China, suna da dadaddiyar al’ada na wasan wuta da harba bindigogi domin wai a fatattaki rashin sa’a na shekara mai karewa, kada su gogawa sabuwar shekara kashin kaji.

A birnin New York na Amurka mutane miliyan biyu aka kiyasta sun fito sanye da manya riguna sanyi domin shaida wannan biki duk da tsananin sanyi da dusar kankara.

Kasashen Afirka ma ba a barsu a baya ba inda a Najeriya kwana aka yi ana shagulgula musamman a birnin Lagos, Jihar da aka ware kwanaki 8 ana bukukuwan tarben wannan rana a bikin da suka yi wa lakabin #Onelagosfiesta.

Duban mutane daga ciki da wajen kasar kan kawo ziyara jihar a wannan lokaci domin gani yadda ake bukukuwan shiga sabuwar shekara musamman wasan wuta da tartsatsi da ake gudanarwa.

Shugabannin Kamaru da Gabon da sauran kasashen duniya sun aike da sakonnin fatan alheri saboda ganin wannan rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.