rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kawo karshen zanga-zangar Iran

media
Dubban jama'ar Iran ne suka tsunduma zanga-zangar don nuna bore kan halin matsin rayuwar da suke fuskanta. Mohammad ALI MARIZAD / AFP

Shugaban Sojin kare juyin-juya halin Iran Mohammad Ali jafari ya ce rashin zaman lafiyar da Iran ke fuskanta tsawon kwannaki sakamakon zanga-zangar da al'umma suka tsunduma ya kawo karshe, inda ya ce Mutum dubu 15 ne kadai suka shiga boren a fadin kasar.


Jafari ya ce an cafke mutane da ke neman tayar da zaune tsaye wanda suka samu horo daga masu neman haddasa rikici a kasar, kuma za a dau matakan da suka dace a kansu.

Tun a makon da ya gabata ne aka fara zanga-zangar a Iran wadda ke da nufin nuna adawa da halin matsin rayuwar da al'umma ke ciki baya ga tabarbarewar tattalin arziki.

Yayin zanga-zangar wadda ita ce mafi muni da kasar ta taba fuskanta tun bayan ta shekarra 2009, inda fiye da mutum 20 suka mutu yayinda aka kame kusan mutum 500 da ake zargi da hannu a tunzura masu zanga-zangar.

Mahukuntan gwamnatin ta Iran dai sun zargi wasu kasashe da tunzura masu zanga-zangar inda suka ce tabarbarewar tattalin arziki kadai ba ta isa ta haddasa makamancin boren ba.