rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Arewa Korea ta Kudu Amurka Donald Trump Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Takunkuman da muka kakabawa Korea ta Arewa sun yi tasiri -Trump

media
Hotunan shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-un. Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sabbin takunkuman da aka sake kakabawa Korea ta Arewa, da kuma matsalolin tattalin arzikin da ta fara fuskanta sun fara tasiri, idan aka yi la’akari da yadda shugaban kasar Kim Jong-un ya nuna bukatar tattaunawa da makociyarsa Korea ta Kudu.


Cikin bayanan da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Trump ya ce yana maraba da matakin na Kim Jong-un duk da cewa, sai da ya ga kasar ta fara fita daga hayyacinta, kafin ya amsa bukatar da aka mika masa da farko.

Tuni dai Korea ta Kudu ta amince da tayin na Korea ta Arewa game da tattaunawar, tare da sanya ranar 9 ga wannan wata na Janairu, a matsayin ranar da tattaunawar zata gudana.

Yayin jawabinsa na shiga sabuwar shekara ne Kim Jong-un ya bayyana amincewa ya tattauna da kasashen duniya kan shirinsu na mallakar makaman Nukiliya, sai dai yace ba gaggawa yake wajen tattaunawar ba, zalika ba rokon kasashen ya ke ba.