Harin bam ya kashe ƴansanda 4 a India
Hukumar ƴansanda a yankin ta ce waɗanda aka kashe sun ci karo da ajalinsu ne lokacin da suke sintiri a wani wuri, mai nisan kilomita 50 daga Srinagar, birni mafi girma a yankin Kashmir da ke ƙasar India
Wallafawa ranar:
Ƴansanda guda 4 ne aka tabbatar sun mutu sa’ilin da wani da ake zargin ɗan tayar da kayar baya ne na ƙungiyoyin Islama ya tayar da bam a yankin Kashmir na ƙasar.
Wannan ne karo na farko da aka samu irin wannan hari a yankin tun bayan kamawar sabuwar shekara.
Kafafen ƴaɗa labaru sun ce an dasa bam din ne a kusa da wani kanti yayin da masu tayar da ƙayar baya suka yi kira da a yi yajin aiki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu