Isa ga babban shafi
Faransa-China

Shugaban Faransa ya soma ziyara a China

A yau Litinin, shugaban Faransa Emmanuel Macron ke fara ziyarar kwanaki uku a China, in da ake sa ran zai kulla wata alaka ta musamman da gwamnatin kasar don yaki da ta’addanci da kuma magance matsalar dumamar yanayi a duniya.

Shugaba Emmanuel Macron da Shugaban China XI Jinping
Shugaba Emmanuel Macron da Shugaban China XI Jinping 法新社
Talla

Emmanuel Macron zai nemi hadin kai daga China don ganin cewa ta taka rawa ta musamman wajen aiwatar da yarjejeniyar birnin Paris da aka cimma don yaki da sauyin yanayi bayan gwamnatin Amurka karkashin Shugaba Donald Trump ta tsame kanta daga yarjejeniyar.

China na daga cikin kasashen da ke fitar da hayaki mai gurbata muhalli a duniya, amma har ila yau, ita ce ta fi kasha makuddan kudin samar da fasahar tsaftace makamashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.