rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Bakin-haure

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Donald Trump ya sanar da daukar sabbin matakai kan yan kasashen waje

media
Donald Trump Shugaban Amurka REUTERS/Carlos Barria

Shugaba Donald Trump ya bayyana baki da ke zuwa kasar daga kasashen Haiti, Salvador da kuma Afirka a matsayin wadanda suka addabi al’ummar Amurka, yana mai alwashin kara daukar sabbin matakai domin hana su shiga kasar.


Trump wanda ke ganawa da wasu ‘yan majalisa daga jam’iyyarsa ta Republican a fadarsa ta White House, ya ce shigar ‘yan asalin wadannan kasashe Amurka lamari ne da ke cigaba da daure masa kai kuma bai dace ba, da dai watakila ‘yan kasashe irinsu Norway ne da ba wani abun damuwa a cikinsa.