rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Amurka Nukiliya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Iran ta yi watsi da batun gyara kan yarjejeniyar Nukiliyarta

media
Jagoran juyi-juya halin Iran Ali Khamenei. Reuters

Iran ta yi watsi da bukatar Amurka na samar da wasu gyare-gyare a yarjejeniyar Nukiliyarta ta shekarar 2015 da ta cimma tsakaninta manyan kasashen duniya.A juma'ar da ta gabata ne Trump ya ce Amurka za ta kara dagawa Iran kafa har na tsawon watanni uku masu zuwa kafin ta sanar da janyewa daga yarjejeniyar ta yadda za ta nemi hadin kan kasashen duniya don gudanar da garambawul akanta.


Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, ta ce bazata amince da duk wani yunkurin jirkirta yarjejeniyar ko kuma sauya mata fasali ba, a yanzu ko kuma a nan gab aba.

Da ta ke maida martini kan kwanaki 120 da Trump ya sanya don kara bibiyar yarjejeniyar a mataki na karshe kamar yadda ya bayyana, Iran ta ce duk wani yunkuri na wargazawa ko illata yarjejeniyar da Donald Trump ke yi ba zai kai ga ci ba.

Trump ya yi gargadin cewa dole ne kasashen turai su mara masa baya wajen aiwatar da gyare-gyare kan kurakuran da ke tattare da yarjejeniyar nukiliyar ta Iran, ko kuma su fuskanci ficewar Amurka daga cikinta.

Trump ya jaddada cewa wannan shi ne karo na karshe da zai daga wa kasar ta Iran kafa, kan kaucewa sake kakaba mata takunkuman, kuma tilas a bi sabbin sharuddan da zai gindaya kan yarjejeniyar, wadda aka cimma domin hana Iran mallakar makamin nukiliya, cikin wa’adin watanni 4.