rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Turkiya Syria Amurka Donald Trump Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Erdogan ya lashi takobin kalubalantar shirin Amurka a Syria

media
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya kalubalanci Amurka kan Syria Reuters/Wolfgang Rattay

Dakarun Turkiya sun ja daga cikin shirin yaki a kan iyakar kasar da Syria domin kalubalantar shirin Amurka na horasda ‘yan tawayen Syria dubu 30 don su narke su zama sojan da za su kare kasarsu.


Shugaban Turkiyan Tayyip Erdogan ya ce zai haifar da gaggarumin cikas a shirin da Amurka ke kokarin aiwatarwa, bayan nuna fushinsa ga Washingoton da ke nuna goyon bayanta ga mayakan Kurdawan Syria.

Gwamnatin Syria da Russia da Turkiya dai sun soki matakin da Amurka ta dauka.

Shugaba Bashar al-Assad na Syria cikin kakausar martani ga Amurkan ya lashi takobin gani bayan dakarun da korar Amurka daga kasarsa.

Assad da ke samun goyan bayan Rasha ya kira shirin na Amurka wani kokari na tarwatsa Syria ta koma karkashin ikon Amurka.