rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Palestine Isra'ila Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta katse tallafin Falasdinu

media
Majalisar Dinkin Duniya na amfani da tallafin Amurka wajen bada agajin gaggawa ga al'ummar Falasdinu euters / Ali Hassan

Amurka ta katse kimanin Dala miliyan 65 daga cikin Dala miliyan 125 da ta ke bai wa hukumar agazawa yankin Falasdinu ta Majalisar dinkin Duniya.


Gabanin wannan lokaci, shugaban Amurka Donald Trump ya ce, akwai yiwuwar kasar ta katse wannan tallafi matukar Falasdinu ta yi watsi da yunkurin samar da zaman lafiya tsakaninta da Isra’ila.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce,matakin zai jefa dubban kananan yara cikin mummunan hali a Falasdinu.

Masharhanta na cewa, matakin zai haifar da nakasu ga yunkurin tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

Ana amfani da tallafin wajen inganta kiwon lafiya da ilimi da kuma bada agajin gaggawa ga al’ummar Falasdinu.

A ranar Lahadin da ta gabta ne, shugaban Falasdinu Mahmud Abbas ya caccaki yunkurin Trump na samar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya , in da ya ce, ba zai amince da duk wani yunkurin na Amurka ba bayan ta ayyana Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

Tuni Isra’ila ta yi madalla da matakin na Amurka.