rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Falasdinawa Isra'ila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta tsayar da ranar mayar da Ofishinta birnin Kudus

media
Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence tare da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu jim kadan bayan kammala wata tattaunawa a Ofishin Firaministan kan batun mayar da Kudus babban birnin Isra'ila yayin ziyarar ta Mr Pence a Isra'ila. Reuters

Amurka ta sanar da cewa nan da karshen shekarar 2019, za ta kammala matsar da ofishin jakadancinta na Isra’ilu zuwa birnin Kudus daga Tel aviv. Mataimakin Shugaban kasar Mike Pence a ziyarar da yanzu haka ya ke ci gaba yi a yankin Larabawa, ya ce zuwa yanzu za su fara matsar da wasu ayyukansu zuwa birnin na Kudus gabanin kammala komawa a 2019.


Mista Pence da ke sanar da haka cikin jawaban da ya gabatar a gaban majalisar dokokin isra’ila a ziyara da ya kai kasar ya bukaci Falasdinuwa da Isra’ila su koma teburin tattaunawa don samar da sulhu kan takkadama da ke tsakaninsu.

Rahotanni sun ce an tursasa ‘yan majalisun Isra’ila Larabawa ficewa daga zaman majalisar lokacin da suka nuna adawa da jawaban mataimakin shugaban na Amurka.

Sanarawar Amurkan na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban Falasdinuwa Mahmud Abbas ya bukaci Kungiyar Tarayar Turai ta amince da yankin Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Mahmud Abbas wanda ke sanar da hakan yayin wata ganawarsa da ministocin kasashen kungiyar a Brussels ya ce yana fatan amincewar ta zamo martini ga Amurka wadda ta yi kunnen kashi da matakin majalisar dinkin duniya da ta bukaci yin watsi da yunkurin na ta na ayyana Qudus din a matsayin babban birnin Isra’ila.

Kusan ilahirin kasashe mambobin majalisar dinkin duniya sun ki amincewa da matakin na Amurka kan mayar da Qudus babban birnin Isra’ila, batun da ya haddasa tashe-tashen hankula a galibin kasashen Musulmai, yayinda a bangare guda ya haddasa asarar rayuka a yankin Falasdinu ta yadda jami’an tsaron Isra’ila suka rika harbe Falasdinawa.