rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Falasdinawa Palestine Isra'ila Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mahmud Abbas na ganawa da EU kan Falasdinu

media
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas AFP/Abbas Momani

Shugaban Falasdinu Mahmud Abbas na shirin gabatar da bukatarsu ga Kungiyar Tarayar Turai ta neman su amince da kasar Falasdinu a matsayin mai cin gashin kanta.


Bayanai na cewa Mahmud Abbas zai gabatar da wannan bukata ce a yau Litinin a birnin Brussels a yayin ganawarsa da ministocin kasashen waje na Kungiyar Tarayyar Turai.

Ministan wajen Falastdinu, Riad al-Malki ya ce, Abbas zai nemi kasashen Turai su dauki matakin ne a matsayin mayar da martini ga shugaban Amurka Donald Trump da ke sanar da amincewarsa da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila.

Kazalika Abbas zai bukaci shugabar diflomasiyar Kungiyar Tarayyar Turai, Federica Mogherini da sauran ministocin nahiyar 28 don ganin cewa sun kara kaimi a rawar da suke takawa wajen samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.