Isa ga babban shafi
EU

EU ta wanke kasashe takwas kan zargin haraji

Kungiyar Tarayyar Turai ta wanke kasashe takwas daga cikin jerin sunayen kasashen da ke taimaka wa attajiran da ke kauce wa biyan haraji a duniya, matakin da ya gamu da suka daga kungiyoyin kare hakkin dan adam.

Ana zargin wasu attajran duniya da boye kudadensu a wasu kasashen don kauce wa biyan haraji a kasashensu na asali
Ana zargin wasu attajran duniya da boye kudadensu a wasu kasashen don kauce wa biyan haraji a kasashensu na asali REUTERS/Yves Herman
Talla

Kasashen da Kungiyar Tarayyar Turai ta wanke sun hada da Panama da Tunisia da Hadaddiyar Daular Larabawa da Mongolia da Macau da Grenada da Barbados .

Kungiyar Oxfam na daga cikin masu rajin da suka caccaki wannan matakin da ministocin kudaden Tarayyar Turai suka dauka na wanke wadannan kasashe daga jerin kasashen da ake kallo a matsayin tudun-mun tsira ga masu kauce wa biyan haraji a duniya.

Masu rajin sun ce, himmar Kungiyar Tarayyar Turai ta tinkarar yaki da kaucewa biyan haraji bayan badakar Panama shakara guda da ta gabata, ta ragu.

Yanzu haka Tarayyar Turai za ta zura ido don ganin yadda wadannan kasashe za su aiwatar da sauye-sauye a dokokinsu na haraji.

Sai dai har yanzu kasashen Amurka da Samoa da Bahrain da Guam da tsibirin Marshal da Namibia da Palau da Saint Lucia da Trinidad and Tobago na ci gaba da kasancewa cikin jerin da EU ta ce, su ne tudun mun-tsira na masu kaucewa biyan haraji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.