Isa ga babban shafi
Brazil

Kotu ta tabbatar da laifin rashawa a kan Lula

Kotun ɗaukaka kara a Brazil, ta tabbatar da laifukan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohon shugaban ƙasar Inacio Lula da Silva, matakin da ya haddasa koma-baya ga aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar a wannan shekara.

Tsohon shugaban kasar Brazil Lula Inacio da Silva.
Tsohon shugaban kasar Brazil Lula Inacio da Silva. REUTERS/Leonardo Benassatto
Talla

Lula wanda ya jagoranci ƙasar daga shekara ta 2003 zuwa 2011 na ɗaya daga cikin waɗanda aka fi sa ran za su lashe babban zaben ƙasar mai zuwa.

Kotun ta yarda da cewa Lula ya karbi miliyoyin kuɗaɗe a matsayin cin hanci daga wani kamfanin gine-gine domin samun kwangila daga gwamnati.

A ƙarƙashin dokokin Brazil, haramun ne duk wani ɗan siyasa da kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukunci kansa bisa zargin aikata ba daidai ba ya tsaya takarar kowane muƙami na shugabancin jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.