rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya Syria Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

MDD na jagorantar tattaunawar Syria a Vienna

media
Staffan de Mistura, jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Syria da ke jagorantar tattaunawar samar da zaman lafiya a kasar a Vienna REUTERS/Pierre Albouy/File Photo

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da sabuwar tattaunawar samar da zaman lafiya a Syria, matakin da kasashen yamma da ‘yan adawa ke fargabar cewa, zai gamu da nakasu saboda Rasha da ta kaddamar da irin wannan yunkuri na diflomasiya.


Sabuwar tattaunawar ta kwanaki biyu a birnin Vienna na zuwa ne bayan gudanar da tattaunawa daban daban har sau takwas a birnin Geneva, amma bangarorin da ke rikici a Syrian ba su samu damar ganawa da juna ba.

Rashin samun nasara a zaman tattaunawar baya, na da nasaba da makomar shugaba Bashl al Assad, in da wakilan gwamnatin kasar suka ce ba za su yi ganawar keke da keke ba har sai ‘yan adawa sun ajiye bukatarsu ta murabus din shugaba Assad daga kujerar mulki.

Tuni Babban wakilin gwamnatin Syria a sabuwar tattaunawar ta yau, Bashar al Jaafari ya isa Vienna don ganawa da jakadan Majalisar Dinin Duniya a Syria, Staffan de Mistura kan wannan batu.

Sai dai bangaren ‘yan adawa ya ce, shi ma zai yi tasa ganawar ce daban da De Mistura a wannan yammaci.

Gabanin zaman na yau, De Mistura ya ce, sabuwar tattaunawar zaman lafiyar na zuwa ne a wani lokaci mai cike da kalubale.

Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean Yves Le Drian ya ce, sabuwar tattaunawar ita ce dama na karshe da ake saran cimma matsayar magance rikicin siyasar shekaru bakwai da ya kashe mutane sama da dubu 340.