rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Donald Trump Zaben Amurka Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zan so na amsa tambayoyi daga masu bincike-Trump

media
Shugaban kasar Amurka Donald Trump tare da na Rasha Vladimir Putin. Sputnik/Mikhail Klimentyev/Kremlin via REUTERS

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce a shirye yake ya amsa tambayoyi daga Robert Mueller, mai bincike na musamman kan katsalandar din ƙasar Rasha cikin zaben Amurka na shekarar 2016.


Lokacin da ya zanta da manema labaru a fadar White House, Trump ya ce zai rantse sannan ya amsa tambayoyin da za a yi masa.

Shugaban na Amurka ya tabbatar da cewa lauyoyinsa na tattaunawa da Mueller kan yiwuwar haɗin baki tsakanin Trump da Rasha wajen yin katsalandan cikin sakamakon zaɓen, da kuma zargin da ake yi masa na kokarin yin zagon-ƙasa ga binciken.

Ya ce zai tattauna da masu binciken da zarar lauyoyinsa suka ba shi izini yin hakan.