Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka za ta fallasa Iran

Amurka ta ce za ta gabatar da gyauron makamai waɗanda ta ce Iran ce ta samar wa ƴan-tawayen Huthi na Yemen.

Jakadiyar Amurka a majalisar dinkin Duniya Nikky Haley.
Jakadiyar Amurka a majalisar dinkin Duniya Nikky Haley. REUTERS/Stephanie Keith
Talla

Jakadiyar Amurka a majalisar ɗinkin duniya Nikkey Haley za ta nuna shaidar ga wakilan ƙasashen kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya, a ƙoƙarin da Amurka ke yi na ganin majalisar ɗinkin duniya ta ƙara takura wa Iran.

Watanni da dama ke nan tun bayan da ƙasar ta Amurka ke bibiyar majalisar ɗinkin duniya wajen ganin ta hukunta Iran, inda har Amurka ɗin ta yi barazanar ficewa daga yarjejeniyar jingine shirin makamin nukila da aka ƙulla da Iran.

Tuni dai Iran ta musanta cewa tana samar wa ƴan-tawayen Huthi makamai, sannan ta bayyana shirin Amurka ɗin a matsayin na bogi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.