Isa ga babban shafi
Afghanistan

Yan bindiga sun kutsa kai cikin wata cibiyar horar da jami’an soji a Kabul

Wa yan bindiga dauke da muggan makamai sun kutsa kai cikin wata cibiyar horar da jami’an soji dake Kabul a kasar Afghanistan, inda suka yi ta dauki ba dadi tsakanin su da jami’an tsaro.

Wasu daga cikin mutanen da suka samu rauni a harin na Kabul
Wasu daga cikin mutanen da suka samu rauni a harin na Kabul Reuters
Talla

Kakakin yan Sandan birnin Bashir Mujahid ya bayyana cewar an ji karar makamin roka da kuma bindigogi a cikin Cibiyar da ake kira Marshal Fahim Military Academy.

Bayanai sun ce an hallaka mutane da dama a harin dake zuwa kwana guda bayan wani kazamin harin da ya hallaka mutane sama da 100 a birnin.

Kungiyar Isil ta sanar da daukar alhakin kazamin harin Cibiyar horar da soji na Kabul a Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.