Isa ga babban shafi
Myanmar

An gano wasu manyan kaburbura makare da gawarwakin ‘yan kabilar Rohingya

Binciken wani Kamfanin  labarai na AP a Amurka ya gano wasu manyan kaburbura makare da gawarwakin ‘yan kabilar Rohingya da sojojin Myanmar suka yi wa kisan gilla.Rahoton da binciken ya wallafa na kunshe da shaidu cikin wadanda suka tsira, da ‘yan uwan matattun da aka hallaka, zalika akwai hotunan bidiyo da ke nuna yadda aka kaddamar da hari a kansu

Yan kabilar Rohingya a kan hanyar su ta zuwa Bangladesh
Yan kabilar Rohingya a kan hanyar su ta zuwa Bangladesh AFP
Talla

‘Yan Rohingya akalla 400 rahotan kaffar labaran AP ya wallafa cewar an aikata kisan gilla a kansu.

Rahotan ya kuma bayyana yada aka bude wuta lokaci guda a kan wasu rukunni maza da ke wasan tamaula a kauyen Gu Dar Pyin.

Wani wanda ya tsallake rijiya da baya a Harin, Noor Kadir, ya ce an hallaka abokan sa 6 tare da bine gawarwakinsu.

Ya kuma kara da cewa ana iya shaida gawarwakinsu ne kawai ta kalar fatansu.

A ranar 27 ga watan Agusta shekara da ta gabata aka kai wannan hari, kamar yadda wadanda suka rayu daga harin suka shaida kuma a cewar su sojojin sunyi kokari boye duk wata shaidar gano laifukan da suka aikata.

Phil Robertson na kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Right ya ce an gano gwan-gwanayen guban Acid da sojoji sukayi amfani da su wajen lalata gawarwaki.

Jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya na musamman da ta jagoranci aikin binciken cin zarafi da kuma kisan da aka yi wa ‘yan kabilar Rohingya a Myanmar, Lee Yang-hee, ta bukaci Majalisar ta aike da wata tawagar masu bincike zuwa kasar domin tantance hakikanin abubuwan da suka faru.

Sojojin Myanmar na ci gaba da ikirarin cewa tana yakar ta’addanci ne, sai dai ‘yan rohingya dake tsallake iyaka domin shiga Bangladesh na bayyana kisan gilla, fyade da konen gidaje da ake aikatawa a kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.