rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Iran Nukiliya China Rasha Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Makaman Amurka ka iya kawar da bil'adama- Iran

media
Kasashen duniya na fargabar yaduwar makamai masu matukar hatsari Defense Ministry/Yonhap/via REUTERS

Kasar Iran ta bayyana cewar sabon shirin gwamnatin Amurka na gina sabbin makaman nukiliya zai dada tabbatar da shirin kawar da bil'adama daga doran kasa.


Wannan matsayi na gwamnatin Iran na zuwa ne bayan da shugaba Donald Trump ya bayyana cewar kasar za ta farfado da makamanta na nukiliya a matsayin mayar da martani kan barazanar da ke kunno kai daga Rasha.

Ministan Harkokin Wajen Iran Mohammed Javad Zarif ya ce, matakin ya saba wa yarjejeniyar kasashen duniya na hana yaduwar makami mai matukar hadari.

Zarif ya ce sabon matsayin na Amurka na nuna dogaro kan makamin nukiliyar wanda hakan babbar barazana ce ga rayuwar jama’a, yayin da ya zargi Amurka da zama bakin-ganga wajen zagon kasa ga yarjejeniyar da kasarsa ta kulla da kasashen yammacin duniya a karkashin Majalisar Dinkin Duniya.

Shi ma shugaba Hassan Rouhani ya bayyana matakin na Amurka a matsayin munafurci.

Kasashen Rasha da China da hukumar da ke hana yaduwar makamin duk sun bayyana damuwarsu akai.