rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tattalin Arziki Amurka Birtaniya Japan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hannayen jari sun yi mummunar faduwa a Duniya

media
Ana saran farfadowar kudaden ruwa a kasuwannin wasu kasashen na duniya amma ban da Japan wadda tattalin arzikinta ya tsaya cak wuri guda, kuma tuni mahukuntn kasar suka yanke tsammanin tashin farashin. REUTERS/John Adkisson

Kasuwannin hannayen jari a kasashen duniya da suka hada da nahiyar Turai da Asiya da Amurka sun yi mummunar faduwa, lamarin da ya haifar da farbagar tsadar kayayyaki a kasashen da abin ya faru.


A tashin farko kasuwannin hannayen jarin sun yi mummunar faduwa a biranen London da Frankfurt da Paris, in da aka samu asarar kusan kashi 3, yayin da a Amurka aka samu asarar kimanin kashi 4.6 a musamman a kasuwar Dow Jones.

Hannayen jarin kasuwar Nikkei ta Japan sun fadi da kashi 4.7, yayin da kasuwar Hang Seng ta rufe akan asarar kashi 5, in da a Korea ta Kudu aka samu asarar kashi 2.6, yayin da a Autralia asarar ta takaita da kashi 3.2.

Ana saran farfadowar kudaden ruwa a kasuwannin wasu kasashen na duniya amma ban da Japan wadda tattalin arzikinta ya tsaya cak wuri guda, kuma tuni mahukuntn kasar suka yanke tsammanin tashin farashin.

Duk da cewa, hannayen jarin a juma'ar da ta gabata sun yi muguwar faduwar da ba a taba ganin irinta cikin ‘yan shekaru a Amurka ba, yanzu haka masu hada-hada sun koma harkokinsu.

Tuni fadar Fadar White House ta bai wa masu saka jari tabbacin samun tagomashi, in da ta ce, ta mayar da hankali kan tsare-tasern bunkasar tattalin arziki na dogon-zango