rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iraqi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

kasar Iraqi ta fitar da sunayen yan ta’addan da ake nema ruwa ajallo

media
Dakarun da ke taimakawa domin tabbatar da tsaro a Iraqi bayan kama wani yankin daga yan kungiyar Isil 路透社

Hukumomin Iraqi sun fitar da jerin sunayen wasu mutane da suka bayyana a matsayin yan ta’addan da suke nema ruwa ajallo, kuma cikin su harda madugun kungiyar IS Abubakar Al-Baghadadi da wasu na hannun damar sa.


Karo na biyu cikin mako guda da hukumomin Iraqi ke fitar da sunayen wadanda take nema ido rufe wadanda galibin su manbobin IS ne da Al-Qa’eda da kuma rusashiyar jam’iyyar Baath ta tsohon shugaban kasar marigayi Saddam Hussein.

Daga cikin sunayen dai akwai sunan shugaban kungiyar IS Abubakar Al-Baghadadi wanda ainihin sunan sa shine Ibrahim Awad Ibrahim Al-Badri Al- Smararrai, da kuma mataimakinsa Abdulrahman Al qaduli wanda aka fi sani da alaa al afari.

Akwai dai sunayen yan usulin kasar Iraq bakwai sai kuma yan Saudi Arabiya biyu, da kuma wasu daga kasashen Jordan da Yemen da Qatar

hukumomin Iraqi na zargin su ne da laifukan daukar nauyin mayakan jihadi da kuma fada a kasar Afganistan

A ranar lahadi ma hukumomin kasar sun fitar da sunayen wasu mutane 60 da ta bayyana da yan ta’adda kuma daga ciki an ga sunan yar tsohon shugaban Kasar Saddam Husaini Wato Raghad wadda ke zaune a kasar jordan

yanzu haka dai akwai akalla mutane fiye da dubu hudu da suka hada da yan kasar Iraqi da na kasashen waje da gwamnatin kasar ke tsare da su a gidajen yari