Kasashe 8 sun bukaci samawa kabilar Rohingya makoma
Faransa, Birtaniya, Amurka da kuma wasu kasashe 5, sun bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya tattauna kan makomar dubban ‘yan gudun hijirar Rohingya da aka kora daga kasar Myanmar.
Wallafawa ranar:
Hakan ya sa Majalisar tasayar da Talata mai zuwa, a matsayin ranar tattaunawa kan matsalar, bayan sauraron rahoto ko bayanin Kwamishinan da ke kula da ‘yan gudun hijira Fillipo Grandi.
Sama da ‘yan kabilar Rohingya 750,000 jami’an tsaron Myanmar suka raba da matsugunin su, sakamakon kisa da fyade da kuma kona gidajen su, abinda ya sa suka tsere zuwa kasar Bnagladesh domin samun mafaka.
Sauran kasashen da suka goyi bayan tattauna matsalar a kwamitin Sulhu, sun hada da Sweden, Poland, Nertherlands, Kazakhstan da kuma Equatorial Guinea.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu