rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Syria Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gabashin Ghouta na fuskantar hadarin yankewar abinci

media
Yankin Ghouta dake karkashin ikon yan tawayen Syria REUTERS/ Bassam Khabieh

Jami’an lafiya sun yi gargadin cewa gabashin Ghouta da ke wajen birnin Damascus ya na fuskantar hadarin yankewar abinci, ruwan sha da kuma magunguna, yayin da kawancen jiragen yakin Rasha da Syria ke ci gaba da luguden wuta kan yankin da ke karkashin ‘yan tawaye.


Yankin Gabashin na Ghouta yana daga cikin yankunan da aka haramta kai hare-hare kan sa a karkashin wata yarjejeniyar tsakanin Rasha, Turkiya gwamnatin Syria da kuma Iran.

Zuwa yanzu sama da mutane 200 suka hallaka yayin da aka shiga rana ta biyar bayan da jiragen yakin Rasha da na Syria suka kaddamar da farmaki kan ‘yan tawaye.