rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jirgin fasinja a Rasha ya yi hatsari

media
Jirgi kirar Antonov na kasar Rasha. ( Photo : Wikimedia.org)

A yau Lahadi wani jirgin Fasinjan Rasha  ya yi hatsari dauke da mutane 71.
Jirgin ya yi hatsari ne dab da birnin Moscow na kasar ta Rasha.

Jami’an agaji sun soma isa a inda  jirgin saman fasinjan kasar Rasha ya yi hatsari .

 


Ofishin hukumar dake sa ido  zuwa batutuwa da suka shafi zirga -zirga jiragen sama ya bayyana cewa babu wata sheida dake nuna  ko jirgin ya samu tangardar na'ura  bayan da ya cira daga filin tashi na Domodedovo.

Jirgin ya kama da wuta kafin ya rufta kasa a wani yanki mai suna  Argounovo  a kudu maso gabacin kasar.

Wannan jirgi kirar Antonov  An-148 na dauke da mutane 71.