rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Isra'ila Falasdinawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta musanta ikirarin Netanyahu kan mamaye yankin Falasdinu

media
Cikin kasa da 'yan sa'o'i da sanarwar ta Netanyahu, Amurka ta musanta ikirarin na sa inda ta ce ko kadan basu taba tattaunawa kan samar da dokar mamaye yankin na Falasdinawa ba. REUTERS/Yuri Gripas

Amurka ta musanta ikirarin da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi na cewa ya tattauna da ita kan wata doka da da za ta bashi damar mallake Yankunan Falasdinawa da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan.Matakin da tuni Kasashen duniya suka fara kallon shi a matsayin yunkurin karshe na rushe duk wani shirin kafa kasar Falasdinu.


Cikin 'Yan sa'o'i da sanarwar ta Benjamin Netanyahu kan shirin mallake Yankunan Gabar Yamma da Kogin na Jordan yayin wata ganawarsa da Yan Majalisu daga Jam’iyyar sa ta Likud, Amurkan ta musanta batun inda ta ce ko kadan basu tattauna makamanciyar maganar da shi ba.

Netanyahu dai ya ce yana shirya daukar matakin ne tare da kasar Amurka, saboda tasirin da take da shi ga kasar Israila.

Wannan mataki dai na zuwa ne kwana guda bayan Firaministan ya hana wasu Yan Majalisu biyu gabatar da irin wannan kudiri a gaban majalisar domin samun amincewar ta.

Masu sa ido kan siyasar Israila sun bayyana cewar daukan irin wannan mataki zai gamu da mummunar suka daga kasashen duniya, ko da yake hakan ba wani sabon abu bane ga Israila.

Tuni Kungiyar Falasdinu ta bayyana shirin a matsayin satar filayen su tare da hadin bakin Amurka.